Daga Bakin Mai Ita tare da Muhibbat Abdulsalam

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo
Daga Bakin Mai Ita tare da Muhibbat Abdulsalam

Muhibbat Abdulsalam tsohuwar tauraruwa ce a Kannywood, wadda yanzu ta rikiɗe zuwa marubuciyar fina-finai.

Ita ce matar babban darakta Hassan Giggs kuma uwar 'ya'yansa uku a tsawon shekara kusan 16 da suka yi tare.

A wannan makon, ta faɗa wa filin Daga Bakin Mai Ita yadda aka yi ta daina fitowa a fina-finan da kuma harkokin da ta mayar da hankali a kansu yanzu.