Mutanen da aka yafe wa azumi da waɗanda za su rama su kuma ciyar
Mutanen da aka yafe wa azumi da waɗanda za su rama su kuma ciyar
Kasancewar addinin Musulunci cike yake da sauki ya sa bayan wajabta azumin Ramadan Sai kuma aka zayyana wasu mutane da kodai aka daukewa azumin Kwata-kwata ko kuma na wucin gadi.
Sheikh Hussaini Zakariyya, limamin masallacin Banex Abuja, ya lissafa kashe-kashen mutanen.
“A mazhabar Malikiyya, an kasa mutane gida uku - wadanda aka daukewa azumin dindindin da wadanda za su rama azumi bayan watan Ramadan da kuma wadanda za su rama azumi tare da ciyarwa.”
Sai dai kuma ya ja kunne cewar duk wanda ba shi da dalilin shan ruwa amma ya sha a watan Ramadan to zai yi kaffara ya azumi 60 sannan ya rama azumin da ya sha din.



