Daga Bakin Mai ita tare da Madam Gloria ta shirin Dadin Kowa

Bayanan bidiyo, Madam Gloria ta shirin Dadin Kowa
Daga Bakin Mai ita tare da Madam Gloria ta shirin Dadin Kowa

Daga Bakin Mai ita na wannan makon ya samun baƙuncin Esther Smart da aka fi sani da Madam Gloria a fitaccen shirin Daɗin Kowa na gidan talbijin ɗin Arewa24.

Ta ce an haife ta ne a Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, amma a Kano ta girma har ta yi karatun boko daga matakin firamare da sakandare har zuwa gaba da sakandare.

Ta ce ita malamar makaranta ce kafin ta shiga harakar fim kuma har yanzu tana aikinta na malanta.