...Daga Bakin Mai Ita tare da Khadija Muhammad

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
...Daga Bakin Mai Ita tare da Khadija Muhammad

Filin ...Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya karɓi baƙuncin tauraruwar fim Khadija Muhammad.

'Yar asalin jihar Kano ce da aka haifa a unguwar Kabuga, kuma ta yi karatun firamare da sakandare a birnin na Kano.

Ta ce ta fara fitowa a wani fim mai suna Dakta Bahijja.

Daga cikin finafinan da ta fito a baya-bayan nan sun ƙunshi: A Duniya, Alaƙa, Gidan Sarauta, Abu a Duhu.

Yanzu haka ɗaliba ce a Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, wadda ake gudanarwa a kwalejin ilimi ta tarayya da ke Kano.