'Haɗa kan mawaƙa ne ya sa aka yi min Sarkin Ƙasidun Bauchi'

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
'Haɗa kan mawaƙa ne ya sa aka yi min Sarkin Ƙasidun Bauchi'

Muhammad Tukur Mato, fitaccen mawaƙin begen Manzon Allah ne da ya yi shuhura a birnin Bauchi da kewaye har ma da shafukan sada zamanta a arewacin Najeriya.

Ya yi waƙoƙi da dama kuma ƙoƙarinsa na ganin an haɗa kan masu bege ne ya sanya har Sarkin Bauchi ya naɗa masa sarautar Sarkin Ƙasidun Bauchi a shekara ta 2022.