...Daga Bakin Mai Ita tare da 'Baban Badaru'

Bayanan bidiyo, Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
...Daga Bakin Mai Ita tare da 'Baban Badaru'

Daga Bakin Mai Ita shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun taurari da mawakan fina-finan Hausa da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood kan abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan kashi na 124, mun tattauna da tauraron fim din nan mai dogon zango, Dadin Kowa, Isa Ibrahim, wanda aka fi sani da Malam Musa tsohon soja ko kuma Baban Badaru.