Shawarar Sheikh Kabiru Gombe ga 'yan Soshiyal Midiya a Ramadan
Shawarar Sheikh Kabiru Gombe ga 'yan Soshiyal Midiya a Ramadan
Watan Ramadan wata ne mai alfarma ga al'ummar Musulmi da ake so su dage da yawan ibada da suka hada da yawan sallah da karatun Alqur'ani da dai sauran ayyukan ibada.
Kan haka ne Sheikh Kabiru Gombe, malamain addinin Musulunci a Najeriya ya ja hankalin masu azumi da su kula dangane da yadda ya kamata suka rinka a amfani da kafafen Soshiyal Midiya.
Ya ce "akwai abubuwa da yawa da za a iya yi da kafafen sada zumunta kamar sauraron tafsiri da dai sauran su."



