Mabiya cocin Angalica da suka yi tawaye kan naɗa mace jagorar cocin na taro a Najeriya

    • Marubuci, Lebo Diseko
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Religion correspondent, Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 4

Cikin wannan mako ne wasu mabiya cocin Anglican masu ra'ayin mazan jiya za su yi wani taro a Abuja domin zaɓen wanda zai zama kishiya ga sabuwar jagorar cocin, waton Archbishop na Canterbury.

Nan gaba ne cikin wannan wata za a rantsar da Sarah Mullally, ƴar asalin Birtaniya a matsayin jagorar mabiya Cocin Angalican ta duniya.

To sai dai naɗin nata ya raba kan mabiya cocin a wasu ƙasashe ciki har da Najeriya.

Mafi yawan Kiristoci masu tsattsauran ra'ayi sun yi imanin cewa maza ne kawai za su riƙa jagorantar cocin.

Babban cocin Vining Memorial da ke birnin Legas ya cika da maza da mata mata waɗanda suka caɓa kwalliya a lokacin ibadar Lahadi na mako-mako.

Sai dai kamar sauran ƙasashen duniya wasu na murna da naɗin Sarah, wasu kuma na adawa da matakin.

Wata da muka tattauna da ita mai suna Bunmi Odukoya, ta ce tana goyon bayan naɗin Sarah a matsayin mace ta farko da za ta jagoranci cocin.

"Aikin Ubangiji, abu ne da kowa zai iya yinsa. Idan ubangiji ya zaɓeka, ba namiji ko mace, duk wanda ubangiji ya zaɓa ya san zai iya,'' kamar yadda ta shaida wa BBC.

To sai dai akwai masu adawa da matakin, kamar Uche Nweke, wadda ya nuna damuwa da batun.

''Wannan ba aƙidar Kiristanci ba ce, Idan ka duba littafin Bayibul da mazanonnin da ubangiji ya aiko, duka babu mace a cikinsu, don haka zaɓar mace a matsayin jagorar babban cocin Anglican a Ingila, ba abu ne mai kyau ba.''

Baya ga kasancewa babbar malama cocin Ingila, ana yi wa Archbishop na Canterbury kallon matsayin babban wakilin ubangiji ga mabiya cocin Anglican kusan miliyan 95 a faɗin duniya.

A taronta na kwana huɗu da ta fara a Abuja ranar Talata, ƙungiyar Gafcon - wadda ta bayyana kanta a matsayin ƙungiyar ''mabiya haƙiƙanin koyarwar ubangiji'' na shirin zaɓar shugaban cocin da za su yi wa mubaya'a, makonni gabanin rantsar da Sarah Mullaly a babban cocin na Canterbury.

To sai dai wasu na ganin matakin na barazanar raba kan mabiya cocin a faɗin duniya.

"Wannan gagarumin raba kai ne, koda ba su so faɗin hakan ba," a cewar Farfesa Diarmaid MacCulloch, ƙwararren masanin tarihi a Jami'ar Oxford da ke Ingila.

"Wannan taro ne da jagororin cocin maza za su je yi a Afirka domin yanke hukuncin da ba zai gamsar da mafi yawan cocinan Anglican ba.''

An ƙirƙiri ƙungiyar Gafcon a 2008, sakamkon bambancin aƙida da aka riƙa samu a cocin, game da auren jinsi.

Rarrabuwar kan ya ƙara zurfafa a shekarun baya-bayan nan, inda a shekarar 2023 ƙungiyar ta yi watsi da jagorancin tsohon shugaban cocin, Hustin Welby, game da shawarar sanya albarka a auren masu neman jinsi, matsayin da wanda ya gada, Dame Sarah ya ɗauka.

Ƙungiyar ta ce tana madana ne da yawun mafi yawan mabiya cocin Anglican na duniya, duk da cewa ana adawa da hakan.

Yayin da ƙungiyar Gafcon ta tara magoya bayanta daga Afirka, ra'ayin nahiyar bai zama iri ɗaya ba.

Alal misali, Cocin Anglican na Afirka ta Kudu da mace ta farko shugabar cocin a Kenya, Emily Onyongo sun taya Sarah Mullally murnar naɗinta.

Kuma yayin da Gafcon ta zargi Cocin Ingila da ci gaba da nuna mulkin mallaka ga sauran majami'un Kudancin Duniya da kuma tilasta bin ra'ayoyinsa na ci gaba, wasu daga cikin waɗanda suka shirya taron na wannan makon sun kasance daga Amurka da Ostiraliya, inda ƙungiyar ke da mabiya.

Zaɓen sabon shugaban cocin zai ƙara kusantar da ita ga ubangiji, ''don haka abu ne da ya kamata a yi'', a cewar Farfesa MacCulloch, wanda shi ma mabiyin cocin Anglican ɗin ne.

Cocin Anglican ta ƙunshi larduna 42 a cikin ƙasashe 165 na duniya. Kowannensu yana da nasa tsarin jagoranci, amma suna aiki da aƙida ɗaya da kuma hanyoyin ibada.

"Muna ganin kanmu a matsayin iyali guda mai cikakken ƴanci,'' in ji Bishop Anthony Poggo, Kamara yadda sakataren cocin Anglican ya shaida wa BBC.

Cocin Anglican ne na uku cikin mafiya yawan mabiya a addinin Kirista, bayan Katolika da cocin Eastern Orthodox.

Coci-cocin da ke ƙarƙashin tafiyar Anglican na tallafawa juna ta fuskar ayyukan ibada da albarkatu ta hanyar abin da aka sani da haɗin gwiwa.

"Wannan duka misali na kyakkyawan koyarwa cocinmu ta fuskar alaƙa,'' a cewar Bishop Poggo.

Za a tattauna shawarwarin faɗaɗa jagorancin Anglican Communion don nuna mafi kyawun yanayin duniya a Majalisar Tuntuɓar Anglican (ACC) a watan Yuni.

Amma wannan yana ɗaya daga cikin abubuwan da Gafcon ta daina yarda da shi, don haka membobinsa ba za su halarci taron ba.

Dangantakar da ke tsakanin cocin Anglican na farko da sauran ƙasashen duniya na ƙara fuskantar haɗari. Amma har yanzu akwai wasu waɗanda ke darajr haɗin kai da Canterbury.

Duk da rashin yarda da ra'ayin Cocin Ingila na sassaucin ra'ayi, matashin Faston nan na Najeriya Alexander Olasinde ya ce alaƙa da Cocin Ingila har yanzu yana da muhimmanci a gare shi.

"Dukkanmu [a matsayin Kiristoci] muna da manufa guda, shi ne samun tsira, don shiga aljanna. Don haka muna buƙatar aƙida ɗaya,'' a cewar faston mai shekara 34.

"Idan muka ci gaba a haka, za mu samu tarin matsaloli, idan kuwa hakan ta faru muka gaza warware matsalolin, ta yaya za mu tsira har mu shiga aljanna?''.