Daga Bakin Mai Ita tare da Humaira ta Daɗin Kowa
Daga Bakin Mai Ita tare da Humaira ta Daɗin Kowa
Ummusalama Abubakar ɗaya ce daga cikin taurarin fim ɗin Daɗin Kowa na tashar Arewa 24.
Haifaffiyar ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano, ta fito a matsayin Humaira a cikin fim ɗin da ta fi sharara da shi, amma ba shi ne fim ɗinta na farko ba.
Ta faɗa wa BBC cewa fitowar da take fara tunawa a fim ɗin ita ce fitowarta ta farko, wadda ta haɗu da Nasir.



