Amsoshin Takardunku 13/04/2025
Amsoshin Takardunku 13/04/2025
A filinmu na Amsoshin Takardunku na wannan makon mun miƙa wa masana daban-daban tambayoyinku domin amsa muku.
Shirin- wanda Umaima Sani Abdulmumin ta jagoranta - ya duba batun yaƙin kasuwanci tsakanin Amurka da sauran ƙasashen duniya, da kuma tasirin hakan kan tattalin arzikin duniya.
Haka ma likita ya yi mana ƙarin bayani kan abin da ke janyo kumburi ga mata masu juna biyu.
Shirin ya ƙarƙare da bayar da tarihin rayuwar fitaccen malamin Addinin Musuluncin nan da ya rasu a makon da ya gabata, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi.