Ganin watan Musulunci a mahangar kimiyya
Ganin watan Musulunci a mahangar kimiyya
Yayin da Musulmin duniya ke dakon watan azumin Ramadan, tuni masana ilimin taurari suka fara yin bayani dangane da al'amuran da suka jibancin ganin wata domin kaucewa rudani.
Simwal Usman Jibril, masanin ilimin taurari ne a Kaduna kuma dan kwamitin ganin watan Musulunci a Najeriya, ya yi bayani a kimiyyance kan al'amarin wata tun daga haihuwarsa har zuwa lokacin da idanu za su iya ganin sa



