Zan kalubalanci sakamakon zaɓen shugaban kasa - Atiku
Zan kalubalanci sakamakon zaɓen shugaban kasa - Atiku
Bayan Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta bayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023, dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben.
Atiku ya ce 'hatta masu sanya ido kan zaben sun san ba a yi shi kan ka'ida ba.'



