Daga Bakin Mai Ita Tare da Gfresh Al'ameen
Daga Bakin Mai Ita Tare da Gfresh Al'ameen
A wannan makon, filin Daga Bakin Mai Ita ya tattauna da Abubakar Ibrahim wanda aka fi sani da GFresh Al'ameen.
An haife shi a jihar Kano, yana kuma da shaidar takardar difloma a bangaren aikin jarida. A cewarsa, ya shiga harkar waka ne shekara bakwai zuwa takwas da suka gabata.
A bidiyon, mawakin ya bayyana ainahin abin da ke tsakaninsa da Sadiya Haruna, wata fitacciyar mai amfani da shafukan sada zumunta. Ya kuma tabo batun rade-radin aure tsakaninsu da ke janyo cece-kuce a kafofin sada zumunta.
Gfresh ya kuma yi bayani kan asalin kalmomin nan na 'Me ya faru?' da yake yawan furtawa a bidiyonsa na shafukan sada zumunta.
Mawakin ya ce ya yi wakoki da dama kuma a ciki bakandamiyarsa ita ce 'Kano to California'.




