Dalilai uku da suka sa duniya ta damu da zaɓen shugaban ƙasar Brazil

A ranar 2 ga watan Oktoba, adadin masu kaɗa ƙuri'a mafi yawa a tarihi za su fita rumfunan zaɓe, wanda masu sharhi ke gani a matsayin "babban gwaji" kan dimokuraɗiyyar ƙasar.

Masu zaɓe fiye da miliyan 150 ne za su zaɓi gwamnoni da kansiloli da 'yan majalisa da sanatoci, amma za a fi mayar da hankali kan zaɓen shugaban ƙasa da za a fafata tsakanin shugaba mai-ci Jair Bolsonaro da tsohon Shugaban Ƙasa Luiz Inacio "Lula" da Silva.

Sakamakon wanan zaɓe mai cike da rarrabuwar kawuna - wanda za a iya samun wanda ya yi nasara ta hanyar shiga zagaye na biyu idan aka rasa wanda ya lashe kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un daga cikin 'yan takara 11 - zai ja hankali a wajen ƙasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Latin Amurka.

Tuni hankalin duniya ya fara karkata, inda har Amurka ta kira gwamnatin Bolsanaro da ta "mutunta salon dimokuraɗiyya" bayan shugaban ya bayyana damuwa game da tsarin jefa ƙuri'a a ƙasar.

Ana sa ran ƙungiyoyin da ke sa ido kan zaɓuka za su hallara a Brazil don bin yadda zaben zai kasance.

Sai dai ba zafin da ake sa ran zaben zai yi ba ne kawai zai sa jama'a su mayar da hankali kan sa ba.

Batun Dajin Amazon

Ana fargaba game da makomar daji mafi girma a duniya yayin wanna zabe, musmaman idan aka duba tarihin manyan 'yan takarar biyu.

Yayin mulkinsa na wa'adi biyu a shekarar 2003-2010, Lula ya rage sare bishiyoyi a dajin na Amazon ta hanyar daƙile haƙar ma'adanai da kiwon dabbobi saboda muhimmancinsa wajen daƙile matsalar sauyin yanayi a duniya.

Duk da cewa an ci gaba da lalata dajin kafin a rantsar da Shugaba Bolsanaro a 2018, amma lamarin ya ƙara ƙamari bayan ya hau mulki a 2019, a cewar rahoton da cibiyar bincike ta Brazil mai suna Institute for Amazon Environmental Research ta fitar.

Lamarin ya ƙara ƙamari da kashi 57 cikin 100 a ƙarƙashin mulkin Bolsanaro, in ji binciken.

Shugaban mai tsaurin ra'ayi ya sha goyon bayan yin ayyukan kasuwanci a dajin na Amazon, kuma ma yana adawa da kare mazauna yankin na gargajiya - shi ne shugaban Brazil na farko tun 1988 da bai taɓa kafa wata doka ba da zimmar kare haƙƙin mazauna yankunan.

"Tuni masana kimiyya suka nuna damuwa cewa Amazon ya shiga wani hali, inda dajin ya kai matsayin da ba zai iya farfaɗo da kansa da kansa ba bayan bala'ai kamar fari da wutar daji da kuma faɗuwar bishiyoyi," a cewar ƙwararre Thais Bannwart yayin hirarsa da BBC.

Brazil na da muhimmanci a siyasance da tattalin arziki

Baya ga matsayinta na ƙasa mafi girma da jama'a a nahiyar Latin Amurka, Brazil na cikin ƙasa 15 mafiya girman tattalin arziki kuma mai faɗa a ji a wasu sassan kasuwanci na duniya.

Brazil ce kan gaba wajen fitar da waken-soya da naman shanu da sinadarin haɗa ƙarfe, sannan kuma babbar abokiyar kasuwanci ce ga Amurka da China. Saboda haka abubuwan da za su faru yayin da kuma bayan zaɓe na da muhimmanci ga ƙasashen duniya.

Masanin harkokin zamantakewa a Brazil, Leonardo Fontes, na ganin matashiyar dimokuraɗiyyar Brazil za ta fuskanci jarrabawa musamman ganin yadda Shugaba Bolsanaro ke ta nuna shakku game da tsarin zaɓen ƙasar na latironi.

Wanda hakan ke sa fargaba cewa magoya bayan shugaban da ake yi wa laƙabi da "Donald Trump na Tropics" ka iya shirya zanga-zangar bayan zaɓe irin wanda aka gani a Amurka ranar 6 ga watan Janairun 2021.

"Dimokuraɗiyyar da ake yi a ƙasashen Yamma na cikin haɗari kuma mu ne muka fi saka ta cikin haɗarin," a cewar Fontes.

"Ya kamata mu kula da abin da Bolsanaro zai yi idan bai samu nasara ba, amma dai za a iya cewa dimokuraɗiyya na fuskantar jarrabawa a Brazil."

Sauyi daga tsattsauran ra'ayi?

Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a a Brazil ta baya-bayan nan da aka gudanar ta nuna Lula ya sha gaban Bolsanaro.

Duk da cewa hakan ba ya nufin tsohon shugaban zai samu ƙuri'un da ba sai an je zagaye na biyu ba, sai dai ana iya cewa masu neman sauyi za su yi nasara kan masu mulki da ke da tsattsauran ra'ayi a zagaye na biyun.

Masana kimiyyar siyasa na ganin irin nasarar da 'yan siyasa masu tsattsauran ra'ayi a duniya - mafi kusa ita ce sabuwar Firaministan Italiya Giorgia Meloni - hakan zai sa a yi fargaba a kowane zaɓe nan gaba.

"Brazil ƙasa ce mai muhimmanci a siyasance da kuma tattalin arziki, saboda haka wannan zai zama koma-baya ga masu tsattsauran ra'ayi," in ji Dr Vinicius de Carvalho, wani masani a harkokin Brazil da nahiyar Latin Amurka a kwalejin King's College London.

"Zaɓen Brazil na zuwa ne a lokacin da ɓangarorin siyasa biyu ke samun nasara a faɗin duniya," a cewar Dr Carvalho yana mai magana kan nasarar da sabon shugaban Colombia ya samu a matsayin mai neman sauyi na farko a tarihin ƙasar a watan Yuni.