Yadda ƴan sanda a China suka lakaɗa wa wakilin BBC duka suka tsare shi

Bayanan bidiyo, Yadda ƴan sanda a China suka lakaɗa wa wakilin BBC duka suka tsare shi
Yadda ƴan sanda a China suka lakaɗa wa wakilin BBC duka suka tsare shi

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Ƴan sandan China sun lakaɗa wa ɗan jaridar BBC duk sannan suka tsare shi na ɗan lokaci.

Sun yi masa hakan ne a yayin da yake aika rahoto kan zanga-zangar adawa da kullen korona da gwamnati ke son yi.

An tsare Ed Lawrence ne a yayin gagarumar zanga-zangar ta ranar Lahadi, aka tsare shi tsawon sa'o'i kafin daga bisani a sake shi.

Gwamnatin China ta ce Mista Lawrence bai bayyana kansa a matsayin ɗan jarida ba.