Lafiya Zinariya: Yadda iyaye za su koya wa yara cin abinci mai inganci

Bayanan sauti
Lafiya Zinariya: Yadda iyaye za su koya wa yara cin abinci mai inganci

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta bayyana muhimmancin cin abinci mai gina jiki, inda ta ce yana bayar da kariya daga kamuwa da cututtukan da ba a ɗauka kamar ciwon zuciya, ciwon suga da kuma cutar sankara.

Hukumar ta kuma bayyana cewa cin abinci iri daban-daban da rage cin gishiri da shan suga da rage cin mai wanda ke daskarewa da kitse da dangogin mai da ake sarrafawa a masana'antu na da matuƙar muhimmanci wajen cin abinci mai inganci.

Haka zalika abinci mai inganci ya ƙunshi haɗa nau'oin abinci daban-daban.

A cikin shawarawari takwas da hukumar lafiya ta Burtaniya, NHS, ta bayar kan cin abinci mai inganci sun haɗa da cin kayan marmari da ganyayyaki, cin kifi sosai, jikin mutum ya zamanto yana da nauyi daidai gwargwado, da daina bari ƙishirwa ta kama ka, da kuma daina ƙin cin karin kumallo, wato abincin safe.

A wannan makon shirin lafiya zinariya ya tattauna da wata likita kuma mai rajin ganin an koma ga cin abincin gida mai inganci, Dr. Hafsatu Sani Zangon Daura ta ce iyaye na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ganin yaransu sun fara cin abinci mai inganci tun suna ƙanana.

Ta kuma yi karin bayani kan hanyar da za su iya bi don cimma hakan.

Sai ku latsa makunnin da ke sama domin sauraron cikakkiyar hirar.