Halin da yaran Gaza ke ciki: An raunata su kuma an kashe iyayensu

    • Marubuci, Dalia Haidar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic

Ma'aikatan lafiya a Zirin Gaza na amfani da wata kalma ta musamman wajen bayyana mutanen da hare-haren Isra'ila suka shafa, kamar yadda aka shaida wa BBC.

"Akwai wani laƙabi da ake amfani da shi a Zirin Gaza na musamman, shi ne WCNSF - wounded child, no surviving family - abin da ke nufin yaron da aka raunata kuma aka kashe iyayensa.

"Kuma ana amfani da kalmar akai-akai," in ji Dr Tanya Haj-Hassan, wanda ke aiki da ƙungiyar Doctors Without Borders a hirarsa da BBC.

Kalmar na bayyana irin halin tashin hankali da yara ke ciki a Gaza. Rayuwarsu kan sauya cikin daƙiƙa - ana kashe iyayensu, da kakanninsu, da 'yan uwansu.

An fara yaƙin ne bayan Hamas ta kai hari cikin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda ta kashe mutum 1,200 kuma ta yi garkuwa da wasu kusan 240.

Hare-haren ramuwar gayya da Isra'ila ta ƙaddamar ya kashe sama da mutum 15,000, ciki har da yara kusan 6,000, a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza.

Marayun da ba su da matsuguni

Ahmed Shabat na ɗaya daga cikin yaran da aka siffanta da WCNSF (yaron da aka raunata kuma aka kashe iyayensa), lokacin da ya isa asibitin Indonesian Hospital a arewacin Gaza yana kuka.

Yaron mai shekara uku ya tsira ne daga wani hari ta sama da Isra'ila ta kai kan gidansu da ke Beit Hanoun a tsakiyar watan Nuwamba. An kashe iyayensa da yayansa a harin.

Cikin ikon Allah ƙananan raunika kawai ya ji. Daga bayan an ce ƙaninsa Omar mai shekara biyu, shi ma ya tsira daga harin kuma sun haɗu bayan an gano ɗaya daga cikin danginsu.

"Bayan harin, mun ji cewa akwai wani yaro a Asibitin Indonesia ba tare da wani ɗan uwansa ba, sai muka garzaya nan take," kamar yadda kawun Ahmed mai suna Ibarhim Abu Amsha ya bayyana.

"Ahmed na tare da wani baƙo. Ya ce an ji wa Ahmed rauni ne a hari ta sama kuma an ceto shi ne mita 20 daga gidan nasu."

Ahmed da Omar yanzu sun zama marayu, waɗanda ba su da gida, babu matsugunin da zai kare su daga hare-hare marasa ƙaƙƙautawa. Saboda haka Ibrahim ya ɗauke su don kulawa da su tare da nasa iyalan.

Da farko ya kai su unguwar Sheikh Radwan amma ya ce sun bar can ɗin bayan "gilasai sun ji wa Ahmed rauni" bayan wani hari.

Sai kuma suka koma sansanin Nuseirat don su zauna a wata makaranta ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD). Amma hatta a sabon gidan ɓuyar da suka koma, an kuma kai musu hari, har ma Ahmed ya sake shiga wani hali.

"Na ruga wajen makarantar na ga Ahmed a gabana a ƙasa babu ƙafafuwansa biyu. Yana rarrafowa wajena, ya buɗe hannayensa yana neman agaji." Haka nan an kashe wani ɗan uwan Ahmed da ke tare da shi a lokacin.

Ibrahim wanda shi ma aka raba su da muhallansu, da ma 'ya'yan 'yar uwarsa, ya ce yana fatan tura Ahmed wajen Gaza don a yi masa aiki. "Ya so ya cimma abubuwa da yawa a rayuwarsa," in ji kawunsa.

"Idan muka je kallon ƙwallon ƙafa sai ya ce yana so ya zama shahararren ɗan ƙwallo."

Kukan neman uwa

Kamar Ahmed, Muna Alwan ma marainiya ce kuma a ajin WCNSF lokacin da ta isa Asibitin Indonesia.

Yarinyar mai shekara biyu ta yi ta kukan neman "mama", amma kuma an kashe mahaifiyar tata.

An zaƙulo Muna ne daga ƙarƙashin ɓaraguzai bayan hari ta sama ya sauka kan gidan maƙwabcinsu a unguwar Jabal Al Rais da ke arewacin Gaza. An kashe iyayen Muna da ɗan uwanta da kakanta. An raunta idonta sosai kuma aka tsaga mata haɓa.

An kai Muna wani asibitin, inda a nan ne gwaggonta Hanaa ta gano ta.

"A intanet muka ga cewa Muna na Asibitin Nasser. Muka je kuma muka gane ta," a cewar Hanaa.

"Kawai tana so ta yi ta kuka, kodayaushe a firgice take, musamman ma idan wani ya matso kusa da ita," in ji Hanaa.

Muna na da yayye mata da ke raye amma suna Birnin Gaza.

"Sun makale a can kuma babu hanyar da za a iya kawo su nan kudanci," kamar yadda Hanaa ta bayyana. "Ina yawan tambayar kaina, me za mu yi? Ta yaya za mu maye gurbin mahaifiyarta?"

'Na rasa ƙafa ta da dangina'

Kwance a kan wani gadon ƙarfe a Asibitin Nasser da ke Khan Younis, Dunya Abu Mehsen mai shekara 11 ta kalli abin da ya rage na ƙafarta ta dama da aka naɗe da bandeji.

Dunya ta tsira daga hari ta sama tare da ɗan uwanta Yusuf da kuma 'yar uwarta bayan makami ya sauka lokacin da suke barci a gidansu da ke unguwar Al Amal a yankin Khan Younis na kudancin Gaza.

Amma iyayenta, da ɗan uwanta, da 'yar uwarta, duka an kashe su. Ta kuma rasa ƙafarta ta dama.

"Lokacin da na ga babana, na firgita saboda yana cikin jini da kuma ɓaraguzai. Mutane na tsaye a kanmu, 'yar uwata kuma tana ta kuka," in ji Dunya. "Na kalli kaina na ga ba ni da ƙafa. Na ji raɗaɗi kuma tunanina kawai shi ne, ta yaya na rasa ƙafa ta?"

"Dunya ba ta san iya lokaci ko kuma yadda aka yi ta isa asibitin ba, amma dai ta tuna cewa ita kaɗai ta je, kuma likitoci suka yi ta tambayarta saboda suna so su gano iyayenta," kamar yadda gwaggonta Fadwa Abu Mehsen ta yi bayani.

Ƙididdigar marayun Gaza

Yanzu abu ne mawuyaci a iya tantance haƙiƙanin adadin marayun da ke Zirin Gaza saboda "tsananin yaƙin da ake yi da kuma yadda lamurran ke sauyawa cikin sauri," a cewar Ricardo Pires mai magana da yawun UNICEF.

Pires ya ce asusun kula da yaran ya yi ƙoƙarin zuwa asibitoci da cibiyoyin lafiya a Gaza don tantance yaran, amma "yunƙurin ba ya sauri saboda ƙalubalen da ake ciki".