Mun raba Najeriya da ƴan ta'adda fiye da 800 a wata uku - Sojoji

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka abin da hedikwatar tsaron ƙasar ta kira "yan ta'dda" smaa da 817 a cikin wata uku.

Haka zalika, sojojin sun ce sun kuɓutar da fararen hula da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su tare da kama ɓata-gari fiye da 1,300 a sassan ƙasar cikin wannan lokaci.

Daraktan yaɗa labaran tsaro a hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba ne ya sanar da haka, lokacin da yake zantawa da manema labarai game da aikace-aikacen dakarun sojin Najeriya cikin wata uku a faɗin ƙasar.

Buba ya ce waɗanda aka kama sun haɗar da masu garkuwa da mutane, su 42 da masu haɗa baki da '‘yan ta’adda' 231, sai ‘yan fashi 33 da ɓarayin shanu 80.

Haka kuma ya ce sojoji sun kama ‘yan bindiga 325 da masu ɓarnata kayan aikin jirgin ƙasa 27 da masu dillancin bindiga 73, da kuma waɗanda ake zargi ɓarayin ɗanyen man fetur ne su 191.

Daraktan ya ƙara da cewa ‘yan ta-da-ƙayar-baya da iyalansu 4,560 ne suka miƙa wuya ga sojoji a yankin Arewa maso Gabas, mai fama da rikicin Boko Haram a cikin wata uku.

Ya kuma ce sojojin sun ƙwato makamai 501 da dabbobi 3,577 da alburusai iri daban-daban har 3,269 da sauran kayan aikin ta'addanci 674.

A yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, Janar Buba ya ce dakarun Operation hadin kai sun kashe ‘yan ta’adda 240 tare da kama mutum 276 da ake zargi masu haɗa baki da su ne, yayin da suka kuɓutar da fararen hula 147 da aka yi garkuwa da su.

Ya ƙara da cewa sojojin sun ƙwato makamai 169 da alburusai iri daban-daban guda 1,195 da sauran kayan aikin ƴan ta-da-ƙayar-baya 199 ciki har da bindigogi ƙirar AK47 guda 57 da bindigar mashinga ɗaya da wata mashingar ƙirar HK21 guda 2.

Akwai kuma wata bindigar ƙirar FN ɗaya da bindigar G3 ɗaya da bindigogin toka 22 da bindiga mai tagwan harsasai guda ɗaya da gurneti uku da kuma kurtun harsasan AK47 guda 73.

A yankin Arewa ta tsakiya kuma, Buba ya ce dakarun Operation Safe Haven sun kashe waɗanda ya kira ‘yan ta'adda 94, tare da kama mutum 477 yayin da suka kuɓutar da fararen hula 76, sannan sun ƙwato makamai iri daban-daban guda 82 da alburusai 760.

Ya ce sojojin Operation Whirl Stroke su ma sun kashe ‘yan ta’adda 83 da kame mutum 104 da ake zargi da kubutar da 18 da aka yi garkuwa da su, tare da kwato makamai 37 da alburusai 68 da kuma kayayyakin aikin ta'addanci guda 127.

A yankin Arewa maso Yamma, Buba ya ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan ta’adda 248, sun kama mutum 116 da ake zargin ‘yan ta’adda ne, tare da kubutar da mutum 359 da aka yi garkuwa da su da kuma kwato jimillar muggan makamai guda 67 da alburusai 926 da sauran abubuwa na muzgunawa 160.

A Kudancin Kudu, ya ce dakarun Operation Delta Safe sun kashe mayaƙa 69, sun kama barayin mai guda 191 da masu hada kai da su, tare da kubutar da mutum 12 da aka yi garkuwa da su.

Bugu da ƙari, ya ce sojojin sun kuma tarbe litar danyen mai sama da miliyan 6 da aka sace da lita sama da miliyan 3 na iskar gas da lita 188,650 na kananzir da kuma lita 65,600 na man fetur.

Ya ce sojojin sun kuma gano tare da lalata jiragen ruwa guda 252 da injinan fanfo 28 tare da kwato makamai iri-iri guda 51.

A yankin Kudu maso Gabas, kakakin rundunar tsaron ya ce dakarun Operation UDO KA sun kashe mayaƙa 80 da kuma kame masu aikata laifukan IPOB/ESN guda 162, ya ce sun kuutar da mutane 109 da aka yi garkuwa da su.

Daraktan ya kuma ce sojojin sun kwato makamai iri-iri guda 63, alburusai guda 320 da sauran abubuwa masu cutarwa guda 166 a cikin wa'adin da aka kammala bincike.