Ku San Malamanku tare da Dr. Dawud Muhammad Abubakar
An haifi Sheikh Dawud Muhammad Abubakar a unguwar Tudun wada cikin garin Gombe ranar 20 ga Janairun 1977.
Malamin ya halarcin makarantar firamaren Karan- Gada, da kuma babbar sakandiren kimiyya ta GSS Gombe. Ya fara karatun shaidar malanta ta NCE a fannin Electrical Electronics Technology Education a FCE, Gombe.
Ya yi digirinsa ta farko kan fannin aikin malanta a Jami'ar Maiduguri. Ya kuma halarci Jami'ar Musulunci ta Uganda.
Dr. Dawud Muhammad Abubakar ya ce ya fara karatun addinin Musulunci a hannun mahaifinsa tun daga kan Kawa'idi da Fiqhu da Iziyyah da Ishimawi da Risalah da kuma Mudawwanatul Kubrah.
Ya ce yana da shekara 11 ya fara yin saukar Alqur'ani duk a hannun mahaifinsa.
Dawud Muhammad Abubakar ya kuma ce ya yi karatu a wajen malamai kamar Mallam Abubakar Muhammad Jos (Mallam Buba) da Mallam Ishaq Zakariyya da Farfesa Isah Ali Fantami da Marigayi Dr Ibrahim Al-khadi, da sauransu da dama.



