Yaron da ya riƙa tonon ɓaraguzai a ƙoƙarin zaƙulo gawar iyayensa a Gaza
Yaron da ya riƙa tonon ɓaraguzai a ƙoƙarin zaƙulo gawar iyayensa a Gaza
Omar yaro ne mai shekara 13 da haihuwa, kuma yana daga cikin ɗaruruwan yara da aka mayar da su marayu a Gaza bayan kashe iyayensu.
An kashe mahaifinsa da mahaifiyarsa a wani harin da Isra'ila ta kai, inda aka bar shi da sauran ƴan'uwansa biyar.
Ƙarami a cikin yaran yana da shekara ɗaya da haihuwa sai kuma babban cikin su mai shekara 17.
Yanzu haka suna zaune ne tare da wani kawunsu, wanda shi ma aka yi raga-raga da gidansa sanadiyyar ruwan bama-bamai da ake yi a yankin na Gaza.



