Manufofin Najeriya biyar kan almajirai da yaran da ba sa makaranta
Manufofin Najeriya biyar kan almajirai da yaran da ba sa makaranta
Hukumar kula da ilimin almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya ta ce a cikin ƴan watanni za a fara ganin ƙoƙarinta na raba miliyoyin yaran ƙasar da jahilci don taimaka musu cimma burinsu na rayuwa idan sun girma.
Hukumar ta nemi haɗin kan iyaye da malaman makarantun allo domin cimma ƙudurinta a ƙasar.
A 2023 ne, aka kafa sabuwar hukumar don inganta rayuwar miliyoyin yaran da ba su da ilimin boko ta hanyar raba su da jahilci da koyar da su sana'o'i, da kakkaɓe talauci, da rashin ji da kuma kantar fatara a tsakanin matasa.
Dakta Muhammad Sani Idris shi ne sabon babban sakataren hukumar, ga kuma ƙarin bayanin da ya yi wa BBC a wannan bidiyo na sama.



